An gano dimbin Black shark a wani yankin ruwa maras zurfi da ke kasar Isra’ila
2021-04-23 15:05:34 CRI
An gano dimbin manyan kifayen teku na Black shark a wani yankin ruwa maras zurfi da ke kasar Isra’ila, wadanda ke iyo a karkashin kwale-kwale. A shekarun nan da suka gabata, dimbin halittun teku na kwarara zuwa wannan yankin ruwa maras zurfi a kasar Isra’ila, sakamakon dumama ruwan tekun da wata masana’antar samar da wutar lantarki ta hanyar kone kwal ta haddasa.