logo

HAUSA

Wang Yi zai jagoranci taron kwamitin sulhun MDD kan rikicin Isra’ila da Palestine

2021-05-16 21:11:29 CRI

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, a yau Lahadi zai jagoranci taron kwamitin sulhun MDD, UNSC, game da halin da ake ciki dangane da rikicin da ya barke tsakanin Isra’ila da Palestine, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana hakan a yau Lahadi.

Kasar Sin, wacce ke jan ragamar jagorancin kwamitin MDDr na karba-karba a watan Mayu, ta sa kaimi ga kwamitin sulhun MDD da ya gudanar da tarukan tuntuba biyu na sirri cikin gaggawa game da batun rikicin da ya kaure tsakanin Palestinu da Isra’ila tare da fitar da jawabin kwamitin MDDr ga manema labarai.

Da take bayyana damuwar kasar Sin game da halin da ake ciki, Hua ta ce, kasar Sin na fatan taron da za a bude yau Lahadi zai tabo batutuwa game da yadda za a ingiza bangarorin biyu su gaggauta tsakaita bude wuta game da yakin da ya kaure a tsakaninsu kana a fara tattaunawar sulhu ba tare da bata lokaci ba.

Ta kuma bayyana fatan da kasar Sin ke da shi ga al’ummomin kasa da kasa, musamman ma kwamitin sulhun UNSC, da su taka rawar gani wajen daidaita yanayin da ake ciki da kuma kokarin warware batutuwan siyasar yankin Gabas ta Tsakiya.(Ahmad)

Ahmad