logo

HAUSA

Me Ya Sa Saukar Na’urar Bincike Ta Kasar Sin A Duniyar Mars Ta Jawo Hankalin Duniya?

2021-05-16 20:29:12 CRI

Kamar yadda tashar Internet ta mujallar wata-wata ta Scientific American ta bayyana ra’ayinta kan samun nasarar saukar na’urar bincike ta Tianwen-1 ta kasar Sin a duniyar Mars a ranar 15 ga wata, saukar na’urar binciken a duniyar Mars, wata sabuwar nasara ce da kasar Sin ta samu yayin da take aiwatar da shirinta a sararin samaniya, lamarin da ya gwada kuzarin kasar Sin wajen yin gwagwarmaya.

Saukar na’urar bincike ta Tianwen-1 mai dauke da karamar na’urar bincike ta Zhurong a duniyar Mars cikin nasara yadda ya kamata daidai inda aka tsara, ta nuna cewa, kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannin binciken sararin samaniya tsakanin duniyarmu ta Earth da wata duniya ta daban, a maimakon duniyar wata kawai.

To, shin ko abu ne mai wuya yin binciken duniyar Mars?

Alkaluman sun nuna cewa, tun bayan da mu ‘yan Adam muka gwada harba na’urar bincike zuwa duniyar Mars karo na farko a shekarar 1960 har kafin saukar na’urar bincike ta Tianwen-1 a duniyar Mars cikin nasara, na’urorin bincike sun samu nasarar shiga iskar da ke kewayen duniyar Mars sau 16 baki daya, amma na’urorin bincike mallakar Amurka sun samu nasarar sauka a duniyar ta Mars tare da fara ayyukan bincike yadda ya kamata sau 9 kawai. Nasarorin da ‘yan Adam muka samu ba su kai rabi ba.

Samun nasarar saukar na’urar bincike ta Tianwen-1 a duniyar Mars, ta shaida cewa, kasar Sin ta iya wasu fasahohi masu sarkakiyya dangane da saukar na’ura a duniyar Mars, musamman ma koda yake wannan shi ne karo na farko da kasar Sin ta fara binciken duniyar Mars. Amma karo na farko ne wata kasa ta samu nasarar zagaya duniyar Mars, sauka a duniyar Mars da kuma yin sintiri a duniya a lokaci guda a duniya baki daya.

Hakika dai, saukar na’urar bincike ta Tianwen-1 a duniyar Mars, ba abin alfahari ne ga kasar Sin kawai ba, har ma yana da muhimmiyar ma’ana ga duk duniya baki daya. Kara fahimtar duniyar ta Mars, yana amfanawa dan Adam wajen kara sanin sirrin sararin samaniya da ma asalin tushen rai, haka kuma yana taimakawa ci gaban duniyarmu, saboda za a fitar da sabbin fasahohi da dama yayin da ake binciken duniyar Mars, wadanda za a yi amfani da su wajen binciken duniyar Mars, tare da yin amfani da su a duniyarmu, a kokarin kyautata zaman rayuwarmu da yanayin aikinmu. Tabbas ne ci gaban da kasar Sin ta samu wajen binciken duniyar Mars zai ba da muhimmiyar gudummowa a wannan fanni. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan