logo

HAUSA

NASA Ta Taya Murnar Nasarar Saukar Na’urar Bincike Ta Kasar Sin A Duniyar Mars

2021-05-16 17:56:23 CRI

Mataimakin hukumar kula da ayyukan sararin samaniyar Amurka wato NASA, Thomas Zurbuchen a jiya Asabar ya aike da sakon taya murnar nasarar saukar na’urar bincike ta kasar Sin mai suna Tianwen-1 a duniyar Mars.

A sakon da ya wallafa a shafin twita, Thomas Zurbuchen ya taya hukumar kula da ayyukan sararin samaniyyar kasar Sin CNSA murna, bisa nasarar da kungiyar kula da ayyukan na’urar bincike ta kasar Sin mai suna Tianwen-1 ta samu inda karamar na’urar bincike ta Zhurong ta sauka cikin nasara a duniyar Mars don gudanar da aikin bincike. A sakonsa ya ce, tare da masanan kimiyyar kasa da kasa, ana fatan aikin zai samar da muhimmiyar gudunmawa ga aikin binciken duniyar Mars don baiwa dan Adam damar kara fahimtar wannan duniya mai launin ja.

Tun da farko a wannan rana, na’urar Tianwen-1 dauke da karamar na’urar bincike ta Zhurong ta samu nasarar sauka a duniyar Mars a karon farko, inda ta isa duniyar mai launin ja, shi ne karon farko da kasar Sin ta cimma nasarar saukar da na’urar bincike a wata duniya ta daban da ba ta shafi duniyar Earth ba.

Wannan shi ne karo na farko a duniya da aka samu nasarar tafiya da kuma sauka a duniyar Mars a lokacin harba na’ura a karo guda, kuma hakan ya baiwa kasar Sin damar zama a sahun gaba a duniya wajen aikin binciken duniyar Mars, a cewar Ye Peijian, wani masanin kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Sin CAS.(Ahmad)

Ahmad