logo

HAUSA

Labarin wata nas ‘yar kasar Sin dake kokarin ba da gudunmowa a kasar Sudan

2021-05-12 14:23:47 CRI

Labarin wata nas ‘yar kasar Sin dake kokarin ba da gudunmowa a kasar Sudan_fororder_nas

Ranar 12 ga watan Mayu rana ce ta musamman da aka kebe domin nuna girmamawa ga nas masu aikin kula da majiyyata. A wannan lokaci na musamman, za mu gabatar muku labarin wata nas ‘yar kasar Sin dake kokarin ba da gudunmowarta a kasar Sudan.

Pu Huiming, wata kwararriyar nas ce a wani asibiti dake birnin Xi’an na kasar Sin. A watan Janairun bana, ta kasance daya daga cikin mambobin tawagar kwararru ma’aikatan lafiya da kasar Sin ta tura zuwa kasar Sudan a karo na 36. Ta ce, “A ranar 15 ga watan Janairun bana, ni da abokan aikina 41, mun tashi daga birnin Xi’an, zuwa garin Guangzhou, daga baya mun isa birnin Alkahira na kasar Masar inda muka canza jirgin sama. A karshe dai mun isa birnin Khartoum, fadar mulkin kasar Sudan, a ranar 16 ga watan Janairun. Wannan shi ne karo na farko da na shiga wata tawagar ma’aikatan lafiya don ba da tallafi ga wasu kasashe.”

Madam Pu ta yi shekaru 17 tana aiki a wani asibitin dake birnin Xi’an na kasar Sin. Bayan da ta samu labarin cewa za a tura tawagar ma’aikatan lafiya ta 36 zuwa kasar Sudan, nan take ta gabatar da bukatar shiga wannan tawagar. A cewarta, “Ni ‘yar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ce, kana na dade ina gudanar da aikin kula da lafiya. Da ma ina son ba da gudunmowa ga aikin da kasar Sin take yi na tallafawa kasashen Afirka a fannin kiwon lafiya. Ko da yake iyalina suna son zama tare da ni, amma dukkansu sun nuna mana goyon baya sosai.”

A watan Afrilun shekarar 1971 ne, kasar Sin ta fara tura tawagogin ma’aikatan lafiya zuwa kasar Sudan. Saboda haka bana, shekaru 50 ke nan, tun bayan da kasar Sin ta kaddamar da aikin tallafawa kasar Sudan a fannin kiwon lafiya. An dora wa hukumar lafiya ta birnin Xi’an aikin daukar kwararrun ma’aikatan lafiya, don kafa tawagar ma’aikatan lafiya irinta na 36 da za a tura zuwa kasar Sudan. Daga baya, hukumar ta zabo kwararrun ma’aitakan lafiya 42 daga asibitoci 20 na wurare daban daban na kasar Sin.

A cikin wannan tawagar musamman, duk likita ko kuma nas na kula da ayyuka daban daban. Misali, Madam Pu tana kula da majiyyata, gami da aikin kudi. Ban da wannan kuma tana taimakawa wajen shawo kan yaduwar wasu cututtuka, aikin da ya shafi daidaita tsarin ayyukansu, da tabbatar da tsabtar muhallin wurin da suke zama. Pu ta kara da cewa, “Yanzu yanayin da ake ciki a kasar Sudan, a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da aikin dakile annobar COVID-19, na da wuya sosai. Mu ma a matsayin mu na ma’aikatan lafiya muna fuskantar tarin kalubaloli.”

A cewar Madam Pu, kayayyakin kiwon lafiya na kasar Sudan ba su da inganci, kana jama’ar kasar ba su lura da matakan kandagarkin annobar COVID-19 yadda ya kamata. Wadannan abubuwa sun sa Madam Pu da abokan aikinta, fuskantar hadarin kamuwa da cutar COVID-19. Ban da wannan kuma, kasar Sudan dake kudancin hamadar Sahara, daya ce daga cikin kasashen da suka fi zafin yanayi, inda birnin Khartoum da suke aikin ake yiwa lakabin “murhun duniya”, saboda tsananin zafin yanayin wurin. Wannan yanayi shi ma ya ba wadannan likitocin kasar Sin wahala sosai.

Duk da haka, Madam Pu da sauran ma’aikatan lafiya na kasar Sin suna kokarin sauke nauyin dake bisa wuyansu, na taimakawa kare lafiyar jama’ar kasar Sudan, gami da Sinawan da suke zama a kasar. Tun lokacin da wannan tawaga ta tashi zuwa Sudan, ta tafi da na’urorin taimakawa numfashi, da na samar da iskar Oxygen, wadanda suka kasance na’urori masu muhimmanci da ake bukata wajen jinyar majiyyata masu kamuwa da cutar COVID-19. Ban da haka, likitocin kasar Sin sun ba da tallafin marufin baki da hanci, da tufafin kariya, da safar hannu, da hula, na musamman, ga asibitocin birnin Khartoum, don taimaka musu tinkarar annobar COVID-19.

A ganin Madam Pu, aikin nas-nas yana da muhimmanci sosai, kuma tana alfahari da wannan aikin da take yi, da yadda take samun damar taimakawa mutane masu bukata a kasar Sin, gami da kasashen Afirka. (Bello Wang)

Bello