logo

HAUSA

An yi wa na’urar binciken duniyar Mars ta farko ta kasar Sin lakabi da Zhurong

2021-04-24 20:51:47 CRI

An yi wa na’urar binciken duniyar Mars ta farko ta kasar Sin lakabi da Zhurong_fororder_微信图片_20210424210041

Yau 24 ga watan Afrilu ranar sararin samaniya ce ta kasar Sin, kuma hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin (CNSA) ta sanar da cewa, an yi wa na’urar binciken duniyar Mars ta farko ta kasar Sin lakabi da Zhurong.

Zhurong sunan ubangijin wuta ne a tsohuwar tatsuniyar Sinawa, wanda kuma ya yi daidai da sunan duniyar Mars cikin harshen Sinanci wato Huoxing, dake nufin duniyar wuta da Sinanci.

A cewar Wu Yanhua, mataimakin shugaban hukumar CNSA, wuta ta kawo da dumi da haske ga magabantan bil adama, kuma ita ce ta haifar da wayewar kan bil adama. Ya ce yi wa na’urar binciken duniyar Mars ta farko lakabi da sunan ubangijin wuta, alama ce dake ingiza yunkurin Sin na binciken duniyar.

Ya kara da cewa, Zhu na nufin fata da Sinanci, wanda ke bayyana kyakkywan fata ga binciken bil adama a sararin samaniya. Rong kuma na nufin dunkulewa da hadin kai, wanda ke haska burin kasar Sin na amfani da sararin samaniya ta hanyar lumana wajen gina al’umma mai makoma ta bai daya ga dukkanin bil adama. (Fa’iza Mustapha)