logo

HAUSA

Xi:JKS tana cika alkawarinta

2021-04-27 21:23:40 CRI

A yau ne, Xi Jinping, babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban kasar, ya ziyarci birnin Nanning dake yankin Guangxi mai cin gashin kansa dake kudancin kasar.

Yayin ziyarar, Xi ya duba kayayyakin al’adu na kabilar Zhuang da aka baje kolinsu, a dakin nune-nunen kayan tarihi dake Guangxi, sannan ya kalli wasannin gargajiya da aka nuna.

Shugaba Xi ya kuma fahimci yadda ake yayata hadin kai da ci gaban kabilu, da karewa da kuma gadon al’adun kabilu. Inda ya ce, Guangxi ta samu babban ci gaba a shekarun baya bayan nan, tare da fitar da al’umma fiye da miliyan 6 da dubu 300 daga kangin talauci.

Kamar yadda ya taba fada, za a fitar da dukkan al’ummar Sin daga kangin talauci, za a kuma fitar da dukkan kabilu daga kangin talauci. Sinawa suna cika alkawarinsu, JKS tana cika alkawarinta, kusoshin JKS suna cika alkawarinsu. Yanzu dukkan al’ummomin kabilu 56 na kasar Sin sun fita daga kangin talauci. Mun cika alkawarinmu. (Ibrahim&Tasallah)

Ibrahim&Tasallah