logo

HAUSA

Xi Jinping ya ziyarci jami’ar Tsinghua

2021-04-19 15:37:33 CRI

A yayin da ake shirin gudanar da bikin murnar kafuwar jami’ar Tsinghua a karo na 110, Xi Jinping, babban jagoran koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar, ya ziyarci jami’ar a yau Litinin 19 ga watan Afrilu. Shugaban ya cimma nasarar duba sashen nazarin fasahar zane-zane, da babban dakin gwaje-gwajen fasaha da dai sauransu, domin kara fahimtar irin girman sauye sauyen da jami’ar ta gudanar, da duba yanayin aikin koyarwa, da bangaren binciken fasahohin kirkire kirkire da sauransu. Daga bisani shugaban ya tattauna da wakilan malamai da dalibai kana ya gabatar da muhimmin jawabi.(Ahmad)