Shugaba Xi ya mika sakon jaje ga takwaransa na Indonesia bisa nutsewar jirgin ruwan yakin kasar
2021-04-27 19:40:56 CRI
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon ta’aziyya ga takwaransa na Indonesia Joko Widodo, bisa nutsewar wani jirgin ruwan rundunar sojojin ruwan kasar.
Cikin sakon da ya aike a Talatar nan, shugaba Xi ya ce ya kadu da jin labarin nutsewar jirgin a teku, lamarin da ya haddasa asarar rayukan jami’ai da dama dake cikin sa.
Ya ce a madadin gwamnati da al’ummar Sinawa, da shi kan sa, yana mika sakon jimamin aukuwar wannan ibtila’i, yana mai fatan iyalan wadanda hadarin ya rutsa da su, za su samu karfin zuciyar jure wannan rashi. (Saminu)