Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki a Liuzhou
2021-04-27 11:04:53 CRI
Jiya Litinin da yamma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki a birnin Liuzhou dake jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta, inda ya ziyarci kamfanin samar da injunan injiniya na Liuzhou da yankin samar da abincin Luo Si Fen wato “taliyar shinkafa dake kunshe da naman snail” bi da bi don fahimtar yadda kamfanoni ke yin kwaskwarima a fannin kirkire-kirkire da bunkasuwar sana’ar samar da kayayyaki da wasu sana’o’in na musamman. Inda ya karawa kamfanonin kwarin gwiwa da su kara karfin yin kirkire-kirkire da dogaro da kansu don ingiza bunkasuwar ’yan kasuwa masu zaman kansu.
An kafa kamfanin samar da injunan injiniya na Liuzhou a shekarar 1958, wanda ya samar da na’urar haka kasa da jigilar kayayyaki ta farko a nan kasar Sin, har zuwa yanzu yana kan matsayin koli na 100 a fannin samar da injunan injiniya a kasar Sin, dake da sassan samar da kayayyaki iri 20 a duk fadin duniya.
Liuzhou mafarin taliyar shinkafa dake kunshe da naman snail wanda ya shahara a yanar gizo. A shekaru 80 na karnin da ya gabata, wannan abinci ya samu karbuwa matuka a Sin, har ya fita zuwa kasashe da yankuna fiye da 20. A shekarar 2020, yawan kudin da aka samu dangane da wannan abinci ya kai Yuan biliyan 11, ya samar da guraben aikin yi fiye da dubu 300. Xi Jinping ya ce, “muna karfafa gwiwar bunkasuwar kamfanoni masu zaman kansu, jam’iyyar JKS da ma kasar na mara musu baya da ba da jagoranci yayin da suka shiga mawuyacin hali da wahalhalu, domin ganin sun samu ci gaba kamar yadda ake fata.” (Amina Xu)