logo

HAUSA

Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ta Taimaka Wa Kasashen Da Ke Aiwatar Da Shawarar Farfado Da Tattalin Arziki

2021-04-20 14:38:59 CRI

Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ta Taimaka Wa Kasashen Da Ke Aiwatar Da Shawarar Farfado Da Tattalin Arziki_fororder_boao

Bayan da kasar Sin ta gabatar da shawarar “Ziri daya da hanya daya” zuwa yanzu, ta kara inganta cudanyar juna a tsakaninta da kasashen da ke aiwatar da shawarar ta fuskar tattalin arziki da ciniki da ma zuba jari. A yayin wani taro dangane da tattara kudade yadda ya kamata a kokarin aiwatar da shawarar, karkashin inuwar taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa ta Asiya ta Boao, wanda aka gudanar a ranar 19 ga wata da yamma, wani jami’in ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya yi karin bayani kan sakamakon da aka samu ta fuskar tattalin arziki da ciniki da kuma zuba jari a cikin shekaru 8 da suka gabata, bayan gabatar da shawarar. Kana kuma, mahalarta taron wadanda suka fito daga kasashen da ke aiwatar da shawarar sun yi nuni da cewa, shawarar ta “ziri daya da hanya daya” ta kawo wa kasashensu damar samun ci gaba, inda kuma za su ci gaba da inganta hadin gwiwa a tsakaninsu da kasar Sin.

Qian Keming, mataimakin ministan kasuwancin kasar Sin ya yi nuni da cewa, bayan gabatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, kasar Sin da kasashen dake aiwatar da shawarar sun samu sakamako a fannonin ciniki da zuba jari. Inda ya ce, “Bayan gabatar da shawarar a shekarar 2013 zuwa yanzu, jimilar kudaden da Sin da kasashen da ke aiwatar da shawarar suka samu daga yin ciniki a tsakaninsu ta kai dalar Amurka triliyan 9.2 baki daya. Sin ta kuma zuba wa kasashen dake aiwatar da shawarar zuba jari kai tsaye da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 136. A cikin shekaru 8 da suka gabata, jimilar kudaden da aka tanada cikin sabbin yarjejeniyoyi tsakanin kasar Sin da kasashen da ke aiwatar da shawarar ya kai dalar Amurka biliyan 940.9, kana yawan kudin da ta samu ya kai dalar Amurka biliyan 638.9 baki daya.”

A shekarar 2020 da ta gabata, duk da yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19, jimilar kudaden da Sin da kasashen da ke aiwatar da shawarar suka samu daga ciniki a tsakaninsu ta karu da kaso 0.7 bisa makamancin lokaci na shekarar 2019. Yawan jarin da Sin ta zuba wa kasashen da ke aiwatar da shawarar kai tsaye ya karu da kaso 18.3 bisa makamancin lokaci na shekarar 2019. Qian Keming ya kara da cewa, duk da yaki da annobar, ana hadin gwiwar zuba jari ba tare da wata tangarda ba karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”. Inda ya ce, “A cikin shekaru 8 da suka wuce, kasashen dake aiwatar da shawarar sun kafa kamfanoninsu guda dubu 27 a kasar Sin, jimilar kudaden da suka zuba a zahiri ta kai dalar Amurka biliyan 59.9. A watanni 3 na farkon shekarar da muka ciki, kasashen da ke aiwatar da shawarar sun kafa sabbin kamfanoninsu 1241 a kasar Sin, adadin da ya karu da kaso 44 bisa makamancin lokaci na shekarar bara. Jimilar kudaden da suka zuba wa kasar Sin a zahiri ta kai dalar Amurka biliyan 3.25, adadin da ya karu da kaso 64.6 bisa makamancin lokaci na shekarar bara. Ma iya ce, duk da illolin yaduwar annobar, yawan jarin da aka zuba tsakanin kasa da kasa ya dan ragu, amma ana hadin gwiwar zuba jari ba tare da wata tangarda ba karkashin shawarar ‘ziri daya da hanya daya’, lamarin da yake da wuyar gani a halin yanzu.”

Tsohon firaministan kasar Pakistan Shaukata Aziz ya bayyana cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya” ta kawo wa kasarsa babbar damar samun ci gaba, Pakistan tana cin gajiya sosai a wasu fannoni, inda ya ce, “Bayan kasar Sin ta gabatar da shawarar ‘ziri daya da hanya daya’, kasarmu ta Pakistan ta fi cin gajiya. Shawarar ta kawo wa kasarmu babban ci gaba wanda ba a taba ganin irinsa a baya ba. Mun kafa tashar jiragen ruwa ta Gwadar, wadda ta kawo wa kasarmu sabbin masana’antu da kuma guraben ayyukan yi. Sannu a hankali garuruwa sun samu ci gaba. Shawarar ta hada mabambantan kasashe tare, za ta kuma ci gaba da kawo mana kyakkyawar dama ta fannonin kasuwa, zuba jari da ci gaba nan da shekaru da dama masu zuwa.”

Kasar Hungary, kasar Turai ce ta farko da ta daddale takardar bayani kan hadin gwiwa ta fuskar shawarar “ziri daya da hanya daya”. Mataimakin shugaban babban bankin kasar Mihaly Patai ya yi bayani da cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya” ta samu babbar nasara. Kuma kasarsa za ta ci gaba da hada kai da kasar Sin karkashin shawarar. Inda ya ce, “Raya tattalin arziki mai dorewa kuma na zamani, sabbin fannoni ne da za su kara azama kan ci gaban tattalin arziki. Kamata ya yi shawarar ta mai da hankali kan wadannan fannoni 2. Kasarmu ta yi farin ciki da shiga shawarar, za mu ci gaba da aiwatar da shawarar yadda ya kamata.” (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan