logo

HAUSA

Sama da wakilai 2,600 zasu halarci taron dandalin Boao na Asiya na wannan shekara

2021-04-18 17:17:37 CRI

Sama da wakilai 2,600 zasu halarci taron dandalin Boao na Asiya na wannan shekara_fororder_1127344121_16187321271971n

Wakilai sama da 2,600, da suka hada da jami’an gwamnatoci, ‘yan kasuwa, da masana daga kasashen duniya da shiyyoyi 60 ne ake sa ran za su halarci taron dandalin Asiya na Boao na wannan shekara(BFA), kamar yadda hukumomi suka bayyanawa taron manema labarai a yau Lahadi.

Ana hasashen nahiyar Asiya zata kasance kashin bayan farfadowar tattalin arzikin duniya a wannan yanayin sauye sauye cikin sauri da duniya ke ciki, a cewar Li Baodong, babban sakataren taron dandalin na BFA, inda ya bukaci a hada gwiwa a yi aiki tare domin cimma nasarar dakile annobar Covid-19, da cike gibin cigaba, da kara dunkulewar tattalin arzikin duniya.

Taron dandalin BFA na wannan shekara zai gudana tsakanin 18 zuwa 21 ga watan nan na Afrilu a Boao, wani gari dake yankin teku a lardin Hainan dake kudancin kasar Sin.

An dai kafa dandalin BFA ne a shekarar 2001. Kungiya ce da ba ta gwamnati ba, kana kungiya ce ta kasa da kasa mai zaman kanta da aka kafa da zummar daga matsayin dunkulewar tattalin arzikin shiyyar tare da kara kusanto da kasashen nahiyar Asiya domin cimma muradun cigabansu.(Ahmad)