logo

HAUSA

Dandalin Boao ya bayyana bukatar karfafa shugabanci a duniya

2021-04-19 14:03:09 CRI

Dandalin Boao ya bayyana bukatar karfafa shugabanci a duniya_fororder_210419-Boao

Tsohon firaministan kasar Faransa Jean-Pierre Raffarin, ya ce dukkan maudu’in taron dandalin Boao na bana, sun fado karkashin shugabanci a duniya.

Tsohon Firaminsitan dake halartar taron dandalin na shekara-shekara dake gudana daga jiya 18 ga wata zuwa ranar 21, ya ce dukkan wani sauyi na bukatar shugabanci mai karfi a duniya, daga matsayin kasar Sin a duniya, zuwa muhimmin aikin Ziri Daya da Hanya Daya, zuwa sabbin dabarun ci gaba da juyin juya halin fasaha.

A cewarsa, dole ne jigon hadin kan kasa da kasa ya zama zaman lafiya. Kuma idan ana son tabbatar da hakan, to ya zama wajibi a inganta tattaunawa da girmama juna. Ya kara da cewa, dole ne kowacce kasa ta taka rawa wajen gina al’umma mai makoma ta bai daya, yana mai cewa yake-yake ko cacar baka, ba za su inganta hadin kai ba, musamman ma a lokacin da ya zama dole kasashen sun kirkiro hulda a tsakaninsu ta karni na 21.

Kungiyar Boao ta kasashen yankin Asiya da aka kafa a 2001, na da burin tabbatar da dunkulewar tattalin arziki bayan matsalar kudin da aka shiga a 1998, kana tana kokarin saukaka musaya tsakanin masu ruwa a yankin Asiya da ma sauran yankunan. (Fa’iza Mustapha)