logo

HAUSA

Tattalin arzikin yankin kudu da hamadar Sahara zai karu da kaso 3.4 a bana

2021-04-16 10:51:41 CRI

Tattalin arzikin yankin kudu da hamadar Sahara zai karu da kaso 3.4 a bana_fororder_129561337_14927663972531n

Asusun ba da lamuni na duniya (IMF), ya ce ana sa ran a samu karuwar tattalin arzikin yankin kudu da hamadar Sahara da kaso 3.4, inda zai farfado daga raguwar da ya yi zuwa kaso 1.9 a shekarar 2020.

A cewar wani rahoton asusun na hasashen tattalin arzkin yankin a bana, farashin kayayyaki da kuma fitar da kayayyaki zuwa ketare, da farfadowar sayen kayayyaki da zuba jari, za su taimaka wajen inganta karuwar tattalin arzikin yankin.

Rahoton ya nuna cewa, a galibin kasashen yankin, ba a sa ran gudunmuwar da kowanne dan kasa ke bayarwa zai koma matakin da yake a shekarar 2019, har sai bayan shekarar 2022, kana kudin shigar da kowanne mutum ke samu, ba zai dawo yadda yake kafin barkewar annoba ba, sai bayan shekarar 2025.

Daraktan sashen kula da Afrika na asusun IMF, Abebe Aemro Selassie ya ce yankin na ci gaba da fama da matsalolin lafiya da na tattalin arziki. Ya bayyana cewa, galibin kasashen na fafutukar yi wa jami’an lafiya da suka kasance kan gaba wajen yaki da annobar COVID-19 riga kafi. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha