logo

HAUSA

Sin ta bada gudunmawar kayayyakin lafiya na yaki da annoba ga UNECA

2021-03-25 10:22:35 cri

Shirin jamhuriyar jama’ar kasar Sin na kungiyar tarayyar Afrika AU, a ranar Laraba ya bayar da gudunmawar kayayyakin lafiya na yaki da annobar COVID-19 ga hukumar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta MDD, UNECA.

Kayayyakin kiwon lafiyar, sun hada da na’urorin gwajin zafin jiki, da injinan samar da iskar oxygen, da rigunan bada kariya, da takunkumin rufe fuska da sauran kayayyakin bada jami’an lafiya kariya (PPEs), wanda aka yi bikin mika kayan a gaban manyan jami’an hukumar ta UNECA da jami’an ofishin diflomasiyyar kasar Sin dake helkwatar hukumar ta UNECA dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

An bayyana gudunmawar a matsayin wani bangare na cigaban hadin gwiwar Sin da Afrika a fannin kiwon lafiya, wanda bangarorin suka kara karfafa shi don yaki da annobar COVID-19, wanda aka bayyana hadin gwiwar a matsayin wata babbar nasara wacce ta baiwa Afrika damammakin samun kayayyakin kiwon lafiyar da take bukata don yakar annobar COVID-19 yadda ya kamata.

Kawo yanzu, kasar Sin ta samar da kayayyakin lafiya na gaggawa ga kusan dukkan kasashen Afrika da kungiyar AU. Kana hadin gwiwar Sin da Afrika wajen samar da riga-kafin annobar yana gudana sannu a hankali.(Ahmad)