CGTN ya fitar da sanarwa game da hukuncin da Ofcom ya yanke kan lasisin reshensa dake Burtaniya
2021-02-05 11:11:57 CRI
Tashar talabijin ta CGTN ta kasar Sin dake watsa shirye-shiryenta ga kasashen duniya, ta bayyana rashin jin dadinta da nuna adawa matuka, kan hukuncin da Ofcom ya yanke na soke lasisin watsa shiryen-shiryen tashar a kasar Burtaniya, da ma yadda Ofcom din ya ki amincewa ya karbi takardar bukatar neman dawo da lasisin tashar.
Tashar wadda a baya ake kira, “CCTV News”, tasha ce dake watsa shirye-shiryenta ga kasashen duniya bisa tsari da kuma kwarewar aikin jarida. Tun lokacin da aka kaddamar da ita a shekarar 2000, CGTN take watsa labarai a sassa daban-daban na duniya, bisa ka’idar nuna gaskiya, da sanin ya kamata da yiwa kowane bangare adalci. Tashar ta kuma himmatu wajen yayata sadarwa da fahimtar juna tsakanin al’ummomin Sin da Burtaniya. Tashar CGTN ta shafe shekaru 18 tana watsa shirye-shirye a Burtaniya, tana kuma karfafa alaka da sauran kafofin watsa labarai da sauran hukumomi dake kasar.
Bugu da kari, tashar CGTN, ta taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa masu sauraronta a kasashen duniya, ciki har da masu kallon shirye-shiryenta a Burtaniya, kara fahimtar kasar Sin da sauran sassan duniya ta fuskoki daban-daban.
A farkon shekarar 2020 ne, biyo bayan munafurcin wasu kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayin rikau da makiyan kasar Sin, suka sa, Ofcom kaddadar da bincike kan lasisin tashar na watsa shirye-shirye a Burtaniya. Sai dai duk da bayanan da tashar ta yiwa Ofcom kan batun dawo mata da lasisinta, amma Ofcom bai kalli kimar tashar a matsayinta na mai watsa shirye-shirye ga kasashen duniya, da kuma nasarori masu yawa da ta cimma, a shekaru 18 da ta shafe tana watsa shirye-shirye a Burtaniya ba, har ma ta yanke hukunci na karshe, ta hanyar fakewa da batun siyasa kan tashar da kafofin watsa labarai na kasar Sin, wajen kin dawo mata da lasisin watsa shirye-shiryen da ta soke.
Bangaren CGTN yana da yakinin cewa, ci gaba da watsa shirye-shiryen talabajin da tashar CGTN za ta yi ga masu kallo da sauraronta a Burtaniya, ya dace da moriyar mazauna Burtaniya. Tashar tana kuma martaba dokoki da ka’idojin kowace kasa tare da watsa labarai da bayanai ga masu kallo da sauraronta dake sassan duniya, bisa adalci, za kuma ta ci gaba da yayata fahimta da sadarwa, da amincewa da juna da yin hadin gwiwa.(Ibrahim)