logo

HAUSA

Kawar Da Kangin Talauci A Kasar Sin, Hanya Ce Mafi Dacewa Wajen Kare Hakkin Dan Adam

2021-04-06 21:56:01 CRI

Kawar Da Kangin Talauci A Kasar Sin, Hanya Ce Mafi Dacewa Wajen Kare Hakkin Dan Adam_fororder_sin

Ranar 6 ga wata, ofishin yada bayanai na majalissar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayani game da aikin da gwamnati ke yi na rage talauci a kasar. Takardar mai taken "Rage talauci: kwarewar kasar Sin da gudummawarta, ta fayyace bayanai game da hanyar da Sinawa suka bi cikin shekaru 100 da suka wuce karkashin shugabancin JKS, wajen cimma muhimmiyar nasarar kawar da matsanancin talauci, da gabatar da salon kasar Sin, tare da raba kwarewarta, da matakai na yaki da fatara, inda abu mafi muhimmanci shi ne har kullum jam’iyyar JKS da ke mulkin kasar Sin tana mayar da al’umma a gaba da kome wajen yaki da talauci. Lamarin da ya sake nuna cewa, kawar da matsanancin talauci, aiki ne mai girma a duniya kana hanya ce mafi dacewa wajen kare hakkin dan Adam.

Bana, JKS mai mulkin kasar Sin take cika shekaru 100 da kafuwa. A duk duniya baki daya, jam’iyyu kalilan ne suka mayar da “kokarin kawo wa jama’a alheri da inganta rayuwar al’uuma” a matsayin babban aikinsu tun daga kafuwarsu, kamar yadda JKS take yi. 

Tun bayan babban taron wakilan JKS karo na 18, a karkashin shugabancin Xi Jinping, JKS ta tsara manyan tsare-tsaren yaki da talauci, ta yi kokari matuka wajen gudanar da babban aikin yaki da talauci, wanda ba a taba ganin irinsa a tarihi ba, kuma ya fi kawo alheri ga al’umma mafi yawa. A ko wace shekara, matsakacin yawan mutanen da aka fitar da su daga talauci ya wuce miliyan 10. Idan ba a kula da jama’a ba, ba a mayar da muradunsu a gaban kome ba, to, ta yaya za a fitar da mutane masu yawan haka daga kangin talauci? (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan