logo

HAUSA

Babbar nasarar da JKS ta cimma cikin shekaru 100 ta zamo abun koyi ga sauran sassan duniya

2021-04-01 20:49:32 cri

Babbar nasarar da JKS ta cimma cikin shekaru 100 ta zamo abun koyi ga sauran sassan duniya_fororder_微信图片_20210401155229

Yanzu haka shirye shirye sun yi nisa, don gane da bikin da kasar Sin ke daf da gudanarwa, na cikar Jam’iyyar Kwaminis mai mulkin kasar shekaru 100 da kafuwa. Ko shakka babu, JKS ce kashin bayan ci gaban da Sin ta samu, inda kasar ta kai ga zama ta biyu a duniya ta fuskar karfin tattalin arziki, kuma kasa mai tasowa ta farko da ta kai ga cimma muhimmin kudurin nan na kawar da fatara, dake cikin ajandar ci gaba mai dorewa na MDD na wannan karni.

Sin ta kuma kafa tarihi, a fannin samun gagarumin ci gaban sassan fasaha, ta zama mai tasiri a fannin karfin soji, da ilimin kwaikwayon tunanin bil Adama, da binciken ilimin likitanci, da raya sana’ar cinikayya ta yanar gizo, da samar da muhimman ababen more rayuwa, da binciken sararin samaniya da dai sauran su.

Don haka, ba abun mamaki ba ne idan an ce jam’iyyar kwaminis, wadda ta jagoranci wannan ci gaba, ta sauke nauyin dake bisa wuyan ta yadda ya kamata, ta kuma nunawa duniya ainihin ma’anar jagoranci na gari, sabanin yadda a wasu kasashe dake tutiya da dimokaradiyya, rayuwar dan Adam ta zama ba a bakin komai ba, balle ma a yi maganar samar da wani ci gaba mai ma’ana.

Wani bangaren na daban da JKS ta zarce sa’a shi ne, duk da yawan al’ummun ta sama da biliyan 1.4, mai kunshe da tarin kabilu daban daban, jam’iyyar ta cimma nasarar hade kan ’yan kasar wuri guda, da irin jagoranci da ya samu karbuwa tsakanin ’yan kasar da sama da kaso 90 bisa dari.

JKS ta yi namajin kokari, wajen tsara salon siyasa da tattalin arziki, mai kunshe da manufofin da ake son cimmawa a lokuta daban daban. Wannan salo ya ingiza damar samar da kudade da albarkatu, da cikakken amfani da su, da kuma auna nasarorin da aka samu.

A wannan gaba da Sin ke kara samun nasarori, kuma JKS ke cika shekaru 100 da kafuwa, masharhanta na ganin a nan gaba, jam’iyyar za ta gamu da karin damammakin raya kasa, da kuma kalubale tattare da hakan.

Ko shakka babu, Sin za ta ci gaba da samun karfi, da kuma matsi na bukatar sauke sabbin nauyaye nauyaye dake wuyanta, na kara inganta rayuwar al’ummar kasa, da ma na cudanyar kasa da kasa. Wannan na nufin baya ga bunkasa ci gaban tattalin arziki, JKS za ta kuma maida hankali wajen wuce matakin kawar da talauci kadai, zuwa sabon matsayi na ingiza Sin, ta yadda kasar za ta rage gibin dake tsakanin al’ummun ta mawadata da matsakaita.

Ko shakka babu, irin wannan aiki mai ban Al’ajabi da JKS ke yi a kasar Sin, zai ci gaba da zamewa sauran sassan duniya darasi, na dabarun samar da bunkasuwa mai dorewa da inganci. (Saminu Hassan)