logo

HAUSA

Kungiyar sada zumunta tsakanin Masar da Sin ta yi bikin cikar JKS shekaru 100 da kafuwa

2021-04-06 12:29:43 CRI

Kungiyar sada zumunta tsakanin Masar da Sin, ta gudanar da wani taron karawa juna sani a ranar Lahadi, domin murnar cikar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin(JKS) shekaru 100 da kafuwa.

Taron dai ya samu halartar kwararrun masana game da kasar Sin dake kasar ta Masar, da marubuta, da jami’an diflomasiyya, da shaihunan malamai dake bincike kan kasar Sin a jami’o’in Masar.

Yayin da yake gabatar da jawabi a taron, tsohon jami’in diflomasiyya, kuma shugaban kungiyar sada zumunta tsakanin Masar da Sin Ahmed Waly, ya ce JKS ta cimma muhimman nasarori, ciki har da yaki da jahilci, da gina manyan ababen more rayuwa, da kawar da fatara, da daidaiton jinsi.

Waly ya ce har kullum, JKS na ingiza sauye sauye da ci gaban a kasar Sin, kuma jam’iyyar da kasar na kara bunkasa tare.

Da yake gabatar da tsokaci ta kafar bidiyo a yayin taron, jakadan Sin a Masar Liao Liqiang, ya godewa Mr. Waly bisa kwazon sa na shirya wannan taro, yana mai jinjinawa zumuncin dake tsakanin Sin da Masar.  (Saminu)