logo

HAUSA

Kaso 90 Cikin 100 Na Sinawa Matasa Sun Bayyana Muhimmancin Sanin Tarihin JKS

2021-04-05 16:07:58 CRI

Wani bincike da jaridar matasan kasar Sin wato China Youth Daily a harshen Sinanci ta gudanar, ya nuna cewa, kusan kaso 90 cikin 100 na Sinawa matasa, suna ganin abu ne mai muhimmanci ga matasa, su san tarihin JKS.

Binciken ya nuna cewa, kaso 82.7 cikin 100 na matasa 2,042 da aka zanta da su, kaso 66.7 daga cikinsu an haife su ne a shekarar 1990 ko bayanta, suna kuma koyan tarihin jam’iyyar ko suna da shirin yin haka.

Haka kuma, sama da kaso 70 cikin 100 na Sinawa matasa, suna fatan sanin tarihin JKS ta kallon shirye-shiryen talabijin, ko muhimman shirye-shirye da nune-nune.

Ma Bin, daya daga cikin matasan da aka tambaya, ya bayyana cewa, ta hanyar sanin tarihin JKS, matasa za su kara fahimtar jam’iyyar da ma kasar baki daya, wato inganta dabi’un da suka dace

A wannan shekara ce, JKS ke cika shekaru 100 da kafuwa. Saboda dora babban muhimmanci kan sani da ma ilimi game da tarihin jam’iyyar, a farkon wannan shekara, kwamitin koli na JKS ya kaddamar da gagarumin gangami, domin karfafawa dukkan mambobin jam’iyya gwiwar shiga a dama da su cikin wannan batu.(Ibrahim)

Ibrahim