logo

HAUSA

Sin: Har Yanzu Xinjiang Na Fuskantar Barazanar Ta’addanci Da Tsattsauran Ra’ayi Duk Da Rashin Kai Wani Hari Cikin Shekaru 4

2021-04-06 20:00:48 CRI

Sin: Har Yanzu Xinjiang Na Fuskantar Barazanar Ta’addanci Da Tsattsauran Ra’ayi Duk Da Rashin Kai Wani Hari Cikin Shekaru 4_fororder_xinjiang

Rahotanni daga kasar Sin na cewa, har yanzu yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa dake yankin arewa maso yammacin kasar, yana fuskantar barazanar ta’addanci da tsattsauran ra’ayi, duk da cewa, ba a kai hare-haren ta’addanci a yankin cikin shekaru hudu da suka gabata ba.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, shi ne ya bayyana haka, lokacin da wakilin CGTN Wu Guoxiu ya tambaye shi game da ko har yanzu batutuwan da suka shafi yankin na Xinjiang, su ne “yaki da ta’addanci da sauya tunanin masu tsattsauran ra’ayi”. Inda ya amsa cewa, haka ne.

Ya yi nuni da cewa, ko da yake yau kusan sama da shekaru hudu ke nan, ba a samu rahoton kai koda hari guda ba, amma yankin yana ci gaba da fuskantar barazana da kalubalen ta’addanci da tsattsauran ra’ayi. Zhao ya kuma bayyana yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa cewa, ya zama wajibi yankin ya ci gaba da daukar matakan yaki da ayyukan ta’addanci da sauya tunanin masu tsattsauran ra’ayi bisa doka.

Jami’in na kasar Sin ya kuma yi karin haske, kan jerin shirye-shiryen CGTN game da yankin na Xinjiang, wanda ya kunshi wasu hotuna masu tayar hankali da ba a taba gani ba da suka faru a yankin da kuma karfin hali na jama’a.(Ibrahim)

Ibrahim