logo

HAUSA

Sin na fatan wasu kasashen yammacin duniya za su mutunta ‘yancin kan jama’ar Xinjiang wajen neman ci gaba

2021-04-02 10:41:45 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a jiya Alhamis cewa, kasar Sin tana fatan wasu kasashen yammacin duniya za su daina nuna fuskoki biyu, da mutunta ‘yancin kan jama’ar jihar Xinjiang ta kasar Sin a fannin neman raya kansu, da kuma girmama kokarin da gwamnatin kasar Sin ta yi wajen samar da karin guraben aikin yi a jihar Xinjiang domin kyautata zaman rayuwar al’umma.

A kwanakin baya, jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta fidda labarin cewa, wani gidan kurkuku na lardin Bas-Rhin dake gabashin kasar Faransa ya samar da “aikin yi” ga wadanda suka aikata laifuffuka, tare da biyansu kudi, lamarin da ya samu yabo matuka bisa yadda wannan gidan kurkuku ya taimaka wa masu laifuffuka a fannin sake neman aikin yi.

Dangane da wannan batu, Hua Chunying ta ce, kasar Sin ta bayyana ainihin abubuwan da suka faru a jihar Xinjiang sau da dama. Yadda aka tabbatar da samar da aikin yi ga al’ummomin jihar Xinjiang ya dace da tsarin mulkin Sin da ma dokokin kasar, ya kuma dace da ka’idojin kwadago da hakkin dan Adam na kasa da kasa. Bugu da kari, ya biya bukatun jama’ar jihar Xinjiang wajen kyautata zaman rayuwarsu, wanda ya kuma samu karbuwa da yabo daga al’ummomin kabilu daban daban na jihar Xinjiang. (Maryam Yang)