logo

HAUSA

Kwalliya ta biya kudin sabulu wajen aiwatar da manufar daidaita harkokin jihar Xinjiang dake kasar Sin

2021-04-02 21:41:34 CRI

Kwalliya ta biya kudin sabulu wajen aiwatar da manufar daidaita harkokin jihar Xinjiang dake kasar Sin_fororder_1

Yau Jumma’a, kafar CGTN dake karkashin tutar babban rukunin rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, ta gabatar da wani shiri mai taken "The war in the shadows: Challenges of fighting terrorism in Xinjiang", wanda ya bayyana tunanin masu tsattsauran ra’ayi, da kalubalen da kokarin kasar Sin ke fuskanta, na dakile ta’addanci a ciki da wajen Xinjiang. Shirin da ya nuna yadda kungiyar ‘yan ta’adda mai suna East Turkestan Islamic Movement ko kuma ETIM a takaice, ta yi yunkurin hura wutar rikici, da yayata tsattsauran ra’ayin addini tsakanin al’ummun jihar Xinjiang, domin kawo baraka da tada zaune-tsaye a jihar.

Ta hanyar kallon shirin bidiyon, za’a iya kara fahimtar cewa, manufofin da gwamnatin kasar Sin ta aiwatar dangane da jihar Xinjiang, sun taka rawa sosai wajen dakile ayyukan ta’addanci, da kare hakkokin al’ummun jihar a fannin rayuwa da samar da ci gaba, wato manufofi ne masu amfani da dacewa da doka, wadanda ya zama dole a aiwatar da su.

Kwalliya ta biya kudin sabulu wajen aiwatar da manufar daidaita harkokin jihar Xinjiang dake kasar Sin_fororder_2

A ‘yan shekarun nan, wasu masu kyamar kasar Sin daga kasashen yammacin duiya, sun rika ruruta wutar rikici kan batun Xinjiang. Kuma ainihin makasudinsu shi ne, boye gaskiyar batutuwan da suka shafi Xinjiang, da tunzura al’ummun kasar Sin daban-daban don su nuna kiyayya da juna, a wani makircinsu na taka birki ga ci gaban kasar Sin baki daya.

Hakikanin gaskiya, batutuwan da suka shafi jihar Xinjiang ta kasar Sin, ba batutuwa ne da suka shafi hakkin dan Adam, ko kabila, ko kuma addini ba, ba haka ba ne sam, batutuwa ne da suka jibanci yaki da ayyukan ta’addanci, da na kawowa kasar Sin baraka.

Sakamakon matukar kokarin da aka yi wajen dakile ta’addanci da kawar da masu tsattsauran ra’ayi, a shekaru hudun da suka wuce, ko aikin ta’addanci daya ma bai auku a jihar Xinjiang ba, kana tattalin arziki da rayuwar al’umma a jihar duk sun bunkasa. Kaza lika mazauna jihar sun fita daga zaman matsanancin talauci tare da sauran sassan kasar Sin.

A wajen taro na 46 na hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya da aka yi kwanan nan, akwai kasashe da dama wadanda suka tsaya ga marawa kasar Sin baya, a aniyarta ta aiwatar da manufofinta kan jihar Xinjiang, gami da karyata jita-jitar da wasu kasashen yammacin duniya suke yi kokarin yadawa. Kuma jakadan kasar Iran dake kasar Sin, wanda a yanzu haka yake ziyara Xinjiang, ya bayyana cewa, ya kamata kowa ya sani, Xinjiang yanki ne mai kwanciyar hankali, kyau da kuma wadata. (Murtala Zhang)