Babban sakataren kungiyar SCO gami da jakadun kasashen waje da dama a kasar Sin sun ziyarci jihar Xinjiang
2021-04-03 17:35:32 CRI
Daga ranar 30 ga watan Maris zuwa ranar 2 ga watan Afrilun bana, babban sakataren kungiyar hadin-kai ta Shanghai ko kuma SCO a takaice, gami da wasu jakadun kasashen waje da jami’an diflomasiyyar kasashe 21 dake kasar Sin, sun kai ziyarar aiki a wasu sassan dake jihar Xinjiang, ciki har da Urumqi, da Kashgar, da Akesu, inda suka binciki yadda ake raya tattalin arziki, da inganta rayuwar al’umma, da kyautata muhallin halittu, gami da tabbatar da ‘yancin bin addini a wurin.
Jami’an diflomasiyyar sun hada da na kasashen Iran, Pakistan, Rasha, Nepal, Azerbaijan, da Armenia, da Tajikistan da Belarus da suransu. Zangon farko da suka yada a jihar Xinjiang, shi ne bikin nune-nunen ayyukan yaki da ta’addanci da kokarin kawar da masu tsattsauran ra’ayi, inda jakadu da dama suka jinjina gami da marawa gwamnatin kasar Sin baya a wannan fanni.
A nasa bangaren, jakadan kasar Pakistan dake kasar Sin, Mista Moin ul Haque ya bayyana cewa:
“Yau na kalli nune-nunen, inda na kara fahimtar tarihin jihar Xinjiang, musamman kara samun fahimtar yadda gwamnatin kasar Sin take kokarin dakile ayyukan ta’addanci da kawar da masu tsattsauran ra’ayi. Ina tare da gwamnatin kasar Sin, don mu shawo kan ta’addanci, wanda shi ne makiyinmu dukka.”
Har wa yau, jami’an diflomasiyyar sun ziyarci wasu wuraren ibada, ciki har da cibiyar karatun Alkur’ani mai girma ta Xinjiang, da babban masallacin dake birnin Urumqi mai suna White Mosque, da masallacin Etigar dake birnin Kashgar, inda suka zurfafa musayar ra’ayi game da aikin horas da malaman addinin Musulunci, da yadda ake gudanar da ayyukan ibada da kuma tabbatar da ‘yancin bin addini na al’umma.
A nasa bangaren, jakadan kasar Iran dake kasar Sin Mohammad Keshavarzzadeh ya bayyana cewa:
“Na ga musulmi a wajen suna zuwa sallah a masallatai daban-daban, wato rahotannin da wasu kafofin watsa labaran kasashen yammacin duniya masu kyamar kasar Sin ke kokarin yadawa game da Xinjiang, ba su da tushe ko kadan balle makama. Ziyarar gani da idonmu na da matukar muhimmanci. Wato ban ga wasu manyan bambance-bambance tsakanin jihar Xinjiang da sauran sassan kasar Sin ba.”(Murtala Zhang)