logo

HAUSA

MDD ta yi Allah wadai da harin ta’addanci a sansanin sojin Somalia

2021-04-05 16:35:51 CRI

Babban wakilin musamman na MDD a kasar Somalia ya yi Allah wadai da harin da sojoji suka dakile wanda aka shirya kaiwa sansanin sojojin kasar Somali (SNA) a garuruwan Barire, da Awdhigle, dake shiyyar kudancin kasar inda sojojin suka yi nasarar kashe ‘yan ta’adda sama da 115.

James Swan, wakilin musamman na babban sakataren MDD a kasar Somalia, ya bayyana cikin wata sanarwa a Mogadishu cewa, wadannan hare hare, wani yunkuri ne na neman mayar da hannun agogo baya game da aikin sake gina Somalia. Ya ce an mika sakon ta’aziyya bisa hasarar rayukan da aka samu, tare da yin addu’ar samun lafiya cikin hanzari ga wadanda suka ji rauni.

Kungiyar Al-Shabab ta sha yin ikirarin daukar nauyin kaddamar da jerin hare-haren wadanda suka haifarwa kungiyar mummunar hasara a yayin da dakarun sojojin gwamnati na SNA ke kara kaimi wajen daukar matakai.

To sai dai kuma, Hassan Haji, ministan tsaron kasar ya bayyana cewa, sojojin SNA su kashe ‘yan bindigar 115 da kama wasu 15 a lokacin harin na ranar Asabar.

Haji, wanda ya ziyarci wani asibiti a Mogadishu domin duba sojojin da suka samu raunuka a hare haren a sansanin sojojin dake shiyyar Lower Shabelle, ya yabawa dakarun sojojin SNA saboda jarumtar da suka nuna da kuma sadaukar da kan da suka yi, yana mai cewa, hanzarin da sojojin suka yi wajen dakile harin ya ceto rayukan jama’a masu yawa.(Ahmad)

Ahmad