logo

HAUSA

Somalia na neman tallafi domin taimakawa mutane miliyan 2.7 dake fuskantar karancin abinci

2021-03-23 13:39:16 CRI

Kasar Somalia ta yi kira ga kasa da kasa, su samar da isassun kudi akan lokaci, domin taimakawa mutane miliyan 2.7 dake fuskantar matsanancin karancin abinci, yayin da ake fama da tsananin fari a kasar.

Khadija Mohamed Diriye, Ministar kula da harkokin jin kai da bala’u ta kasar, ta ce tasirin ambaliya da farin dango da ma na annobar COVID-19, sun kara jefa mutane miliyan 2.7 a fadin kasar, cikin matsalar jin kai.

Ta bayyana cikin wata sanarwa da aka fitar a Mogadishu cewa, yanayin karancin abincin abun damuwa ne, kuma idan masu bada agaji basu gaggauta kara ayyukansu a wasu wuwaren da a baya suka fuskanci fari ba, to lamarin zai yi mummunan tasiri kan miliyoyin jama’ar kasar. (Fa’iza Mustapha)