logo

HAUSA

Sakatare Janar na MDD ya bayyana damuwa game da barkewar rikici a babban birnin Somalia

2021-02-20 17:06:39 CRI

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya bayyana matukar damuwa dangane da barkewar rikici a Mogadishu babban birnin kasar Somalia, inda ya yi kira ga dukkan bangarori masu ruwa da tsaki, su kai zuciya nesa.

Wata sanarwa da mataimakin kakakinsa, Farhan Haq ya fitar, ta ruwaito Antonio Guterres na cewa an ji amon harbe-harbe da makaman roka a titunan Mogadishu a jiya Juma’a, yayin da rikici ya barke tsakanin jami’an tsaro da magoya bayan bangaren adawa dake zanga-zangar kin amincewa da jinkirta zaben kasar. (Fa’iza Mustapha)