logo

HAUSA

AU ta jinjinawa rawar da dakarun kiyaye zaman lafiya mata ke takawa a Somalia

2021-03-09 10:27:20 CRI

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika a kasar Somalia (AMISOM), ta jinjinawa dakarun wanzar da zaman lafiya mata bisa rawar da suke takawa a aikin kiyaya zaman lafiya da kuma tabbatar da tsaro a yankunan kasar ta kahon Afrika.

Francisco Madeira, wakiliyar musamman ta hukumar gudanarwar AU a  Somalia, kana jagorar tawagar AMISOM, ta kuma yabawa ci gaban da gwamnatin Somalia ta cimma kawo yanzu wajen samarwa mata ayyukan dogaro da kai, da kara baiwa mata damammakin shiga a dama da su a harkokin siyasa, da kuma baiwa mata kariya daga fuskanci keta hakki da cin zarafinsu ta hanyar lalata.

Madeira, ta bayyana cikin sakon taya murnar zagayowar ranar mata ta duniya cewa, tana kara jinjinawa jami’an tsaro mata dake aiki a hukumomin tsaro a Somalia da kuma masu aiki a tawagar wanzar da zaman lafiya ta AMISOM, wadanda suka sadaukar da rayuwarsu, domin cimma nasarar farfadowar zaman lafiya da tsaro a kasar Somalia da Afrika baki daya.(Ahmad)