logo

HAUSA

Kasashen Yammacin Duniya Sun Kau Da Kai Daga Cocoa Da Suke Samu A Yammacin Afirka

2021-04-02 09:55:10 CRI

Kasashen Yammacin Duniya Sun Kau Da Kai Daga Cocoa Da Suke Samu A Yammacin Afirka_fororder_auduga

Kasashen Yammacin Duniya Sun Kau Da Kai Daga Cocoa Da Suke Samu A Yammacin Afirka_fororder_coco

A ’yan kwanakin baya, batun Xinjiang ya jawo hankalin akasarin ra’ayoyin jama’a sosai. Da farko dai wasu kafofin yada labaru na kasashen yammcin duniya sun shafa wa jihar Xinjiang kashin kaji, sa’an nan kasashen yammacin duniya sun sanyawa kasar Sin takunkumi dangane da “batun Xinjiang” da a hakika dai babu irin wannan batu, daga baya kuma wasu kamfanonin kasashen yammacin duniya sun kauracewa sayen audugar Xinjiang. Hankulan wasu ’yan siyasa da wasu ’yan kasuwa na kasashen yammacin duniya sun karkata kan yadda wai aka tilasta wa mutane yin aiki a wasu wurare na duniya, amma sun kau da kai daga yadda kamfanoninsu suka tilasta wa kananan yara yin aiki a yammacin Afirka.

A shekaru fiye da goma da suka wuce, an sha sukar kamfanin Nestle da laifin yin hayar kananan yara su yi aiki a gonkin Cocoa a kasashen ketare, wadanda suke samar wa kamfanin waken Cocoa. Ya zuwa yanzu a kasashen Kodivwa da Mali da sauran sassan duniya, kananan yara matalauta miliyan 1 da dubu 560 ne suke aikin karfi mai wahala matuka. Wasu daga cikinsu shekarunsu ba su wuce 6 a duniya ba. A kowane mako wadannan kananan yara suna shafe kwanaki 6 suna aiki, inda suke aiki har sa’o’i 14 a kowace rana. Suna barci a kananan gidaje a dab da bishiyoyin Cocoa da dare. Suna shan gurbataccen ruwa daga tabki. Albashinsu a kowane mako dalar Amurka 9 ne kawai. Wasu kuma suna aiki ba tare da samun kudi ba. A wasu lokuta idan ba su yi aiki tukuru ba, to, a kan doke su, kana kuma masu gadi dauke da makamai suna sa musu ido a ko da yaushe.

A shekarar 2001 ne kamfanin Nestle da sauran manyan kamfanonin irinsa sun san yadda ake hayar kananan yara su yi aiki a wasu kasashen yammacin Afirka, sun yi shelar cewa, za su daina yin amfani da waken Cocoa da kananan yara suka girbe. Sun kuma sa hannu kan yarjejeniyar Harkin-Engel, inda aka bukaci a daina yin hayar kananan yara kafin shekarar 2005, amma har yanzu, kananan yara suna aikin wahala a filayen noman bishiyoyin Cocoa a yammacin Afirka.

Masu karatu, shin kun gane? Kasashen yammacin duniya sun kau da kai kan yadda aka yi hayar kananan yara su yi aiki a filayen noman bishiyoyin Cocoa a yammacin Afirka. Amma yayin da aka yada karya da neman bata sunan audugar Xinjiang, wadannan kasashe sun nuna halayyarsu ta munafurci, inda suka soki jihar Xinjiang da ma kasar Sin. Sun kau da kai daga hakikanin shaidu, sun dora wa kasar Sin laifi bisa karyar da aka yada. Ba su kula da hakkin dan Adam ba, ba su kula da ’yan kananan kabilu ba. Ba su kula da jin dadin rayuwar kananan yara ba. Abin da suke mai da hankali a kai shi ne yaya za su iya bin sawun gwamnatocinsu wajen bata sunan Xinjiang da kuma hana bunkasar kasar Sin. Wannan ne babban burin da kasashen yammacin duniya suke son cimmawa.

Kowa ya ga yadda kamfanonin Nestle da H&M ba sa jin kunya, inda suka nuna halayyarsu ta munafunci. Babu abin da suke, illa kokarin mayar da kasashen duniya wawaye da makafi. Duk da haka a wannan karo, al’ummar kasar Sin ba su yarda da haka ba. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan