logo

HAUSA

Dalilin da ya sa ake yada jita-jita game da audugar da ake samarwa daga Xinjiang

2021-03-31 13:31:30 CRI

Dalilin da ya sa ake yada jita-jita game da audugar da ake samarwa daga Xinjiang_fororder_20210331-bayani-Bello

Yanzu haka wasu kamfanonin kasashen Turai da Amurka sun ce ba za su ci gaba da sayen audugar da ake samarwa daga jihar Xinjiang ta kasar Sin ba, bisa dalilin wai gwamanatin kasar Sin tana tilastawa ‘yan kwadago aiki a jihar. Amma a hakika wannan dalilin da aka bayar, jita-jita ce kawai da makiyan kasar Sin suke yadawa kan jihar Xinjiang ta kasar Sin.

Wadannan kamfanonin da suka ki yin amfani da audugar jihar Xinjiang, sun ce sun dauki matakin ne bisa shawarar da kungiyar tabbatar da ingancin auduga ta BCI dake kasar Switzerland ta yanke. Sai dai game da kungiyar BCI, wasu kafofin watsa labaru sun riga sun yi bincike kan asalinta sosai, inda aka ce, ko da yake kungiyar ba karkashin gwamnati take ba, amma kungiyar tana karbar kudi daga wasu bangarori a kai a kai, ciki har da hukumar raya kasashe ta kasar Amurka (USAID), wadda ta dade tana neman yin tasiri a fannin siyasa kan sauran kasashe. Sanin haka ya sa ya dace jama’a su rika fahimtar dalilin da ya sa kungiyar BCI ke daukar wasu matakai, inda ta yi biris da rahoton da reshenta dake birnin Shanghai na kasar Sin ya gabatar, cewa ba a gano shaidar tilastawa mutane aiki a Xinjiang ba, kana ta dauki wani mataki ne bisa rahoton na karya, da cibiyar nazarin manyan tsare-tsare ta kasar Australia ta gabatar, wadda ta dade tana adawa da kasar Sin.

Hakika idan mun waiwayi jita-jitar da kasashen yammacin duniya suke kokarin yadawa game da jihar Xinjiang ta kasar Sin, da yadda suka kakabawa kasar Sin takunkumi, to, za mu iya fahimtar cewa, yadda ake kokarin alakanta audugar Xinjiang da batun “tilastawa mutune aiki”, shi ma wata jita-jita ce da aka kirkiro, bisa wani tsari na musamman: Inda da farko wasu masana ko kuma cibiyoyin nazari masu adawa da kasar Sin sun kirkiri wani rahoto maras tushe dangane da jihar Xinjiang, daga baya manyan kafofin watsa labarai irinsu BBC da CNN, suka tsamo rahoton tare da kokarin yada shi, ko da yake akwai kurakurai da yawa a ciki. Kana a nasu bangare, ’yan siyasan kasashen yammacin duniya sun yi kokarin gabatar da matakin kakabawa kasar Sin takunkumi.

Sai dai mutanen da suke kokarin kirkiro har ma da yada jita-jitar, sun yi watsi da shaidu na gaskiya, wato: Tuni an fara yin amfani da na’urorin na zamani masu tarin yawa, wajen tsintar auduga a jihar Xinjiang ta kasar Sin, don haka ba a bukatar ’yan kwadago da yawa. Alkaluman da aka gabatar sun nuna cewa, a shekarar 2020, an yi amfani da na’urorin zamani wajen tsintar kashi 70% na audugar jihar Xinjiang. Yayin da wasu kuma ke maganar wai ana “tilasta mutane aiki”, ko suna nufin “tilastawa na’urori aiki” ne?

Kana sana’ar samar da auduga ta riga ta zama ginshikin tattalin arzikin jihar Xinjiang, wanda ke taka muhimmiyar rawa a fannin kyautata zaman rayuwar jama’ar jihar, ciki har da al’ummar Uygur. Saboda haka muna iya ganin wani yanayi na sabani da kai ne cikin matakan da wasu ’yan siyasan kasashen yammacin duniya suka dauka, inda a hannu guda, sun nuna tamkar suna karkata ne ga batun hakkin dan Adam na jihar Xinjiang sosai, yayin da a daya hannun kuma, suna neman mayar da audugar jihar Xinjiang saniyar ware, tare da matsawa kamfanonin da suka dauki ma’aikatan ’yan wasu kabilu na jihar Xinjiang lamba.

Idan mun yi bincike kan manufar kasashen yammacin duniya dangane da jihar Xinjiang ta kasar Sin sosai, za mu fahimci ainihin abun da suke kokarin cimmawa.

Sanin kowa ne cewa, a baya jihar Xinjiang ta fuskanci hare-haren ta’addanci. Sai dai wasu nagartattun matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka, sun dawo da harkokin tsaro da kwanciyar hankali a jihar, inda ba a sake samun abkuwar harin ta’addanci ba cikin shekaru 4 da suka wuce, kana tattalin arziki da zaman rayuwar jama’a sun inganta sosai a jihar. Sai dai, wasu mutane masu adawa da kasar Sin ba su son ganin ci gaban jihar Xinjiang. Maimakon haka suna neman kara tayar da rikice-rikice a jihar, don hana kasar Sin samun ci gaba. Saboda haka suna fakewa da maganar audugar jihar Xinjiang, don neman haifar da cikas ga yunkurin ’yan kabilar Uygur na jihar na raya harkoki da samun guraben aikin yi, ta hanyar raunana yanayin tsaro na jihar. (Bello Wang)

Bello