logo

HAUSA

Burin masu neman bata sana’ar noman Audugar yankin Xinjiang ba zai cika ba

2021-03-31 09:35:54 CRI

A cikin ’yan kwanakin nan, masu adawa da gwamnatin kasar Sin dake yammacin duniya, suna ci gaba da yada jita-jita cewa, wai “ana tilastawa al’ummomin jihar Xinjing aikin shuka da ma tsinkar auduga”, har ma wasu daga cikinsu, suka kakabawa wasu daidaikun Sinawa da kamfanonin kasar takunkumi haka kawai. Sai dai ita ma kasar Sin ta mayar da martani kan wasu daidaikun mutane da kamfanoni makiya kasar Sin kan wannan batu.

Burin masu neman bata sana’ar noman Audugar yankin Xinjiang ba zai cika ba_fororder_20210331世界21011-hoto2

Bisa bayanin da hukumar kula da harkokin gona ta jihar Xinjiang ta kasar Sin ta fitar, ana gudanar da kashi 69.83 bisa dari na aikin tsinkar auduga da na’urori a duk fadin jihar Xinjiang, kuma wannan adadin ya kai kaso 95% a arewacin jihar.

Mutanen jihar Xinjiang sun wallafa hotuna da bidiyo da dama game da yadda suke gudanar da aikin tsinkar auduga. A cikin hotunan, an ga yadda motar tsinkar auduga take aiki ba tare da mutane a cikin gonar ba. Don haka, batun ana wai kashi 70% na audugar Xinjiang ana girbe su da hannu ba gaskiya ba ne.

Burin masu neman bata sana’ar noman Audugar yankin Xinjiang ba zai cika ba_fororder_20210331世界21011-hoto1

Ban da haka kuma, aikin tsinkar auduga, aiki ne dake samar da kudin shiga masu yawa ga mutanen jihar Xinjiang, har wasu mutane daga sassan kasar Sin su kan tafi jihar Xinjiang domin gudanar da wannan aiki.

A kimanin kwanaki 50 na tsintar auduga a kowace shekara, mai aikin tsintar auduga na iya samun albashin da ya kai Yuan sama da dubu 10 (kwatankwacin dalar Amurka 1550 ko fiye), shi ya sa, babu bukatar a tilastawa wani ko wata yin wannan aiki.

Sana’ar auduga babbar sana’a ce dake samar da wadata ga al’ummomin jihar Xinjiang,a don haka, gwamnatin kasar Sin za ta dukufa wajen inganta wannan sana’a domin kare al’ummomin jihar Xinjiang. Idan ’yan siyasar yammacin duniya suka ci gaba da yada jita-jita game da jihar Xinjiang, babu shakka ita ma kasar Sin za ta mayar musu da martanin da ya dace. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)