logo

HAUSA

Namibia za ta karbi rancen dala miliyan 100 daga bankin AfDB

2021-03-25 10:28:48 CRI

Kasar Namibia za ta karbi rancen dalar Amurka miliyan 100 daga bankin raya Afrika na AfDB, domin taimakawa ayyukan shugabanci da farfado da tattalin arziki.

Kakakin ma’aikatar kudi ta kasar Tonateni Shidhudhu, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, bukatar da aka gabatarwa bankin AfDB a watan Yunin shekarar 2020, ya samu amincewar daukacin mambobin hukumar daraktocin bankin a ranar 17 ga wata a shekarar 2021 da muka ciki, a matsayin rancen kudin aiwatar da harkokin shugabanci da shirin farfado da tattalin arzikin kasar.

Ya ce an amince da bayar da rancen ne bayan kammalawar shirin raya tattalin arziki da ya gudana tsakanin shekarar 2017 zuwa 2020, wanda ya samu dimbin sakamako a bangarorin rage gibin kudi da basussukan gwamnati da tafiyar da dukiyar al’umma da inganta yanayin kasuwanci. Sai dai, annobar COVID-19 na barazanar mayar da hannun agogo baya. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha