logo

HAUSA

Namibia ta bude tallar neman wadanda za su iya samar mata alluran COVID-19

2021-03-16 14:12:23 CRI

Ma’aikatar lafiya da ofishin hulda da suka shafi hidimomi na jama’a na kasar Namibia, suna kira ga kamfanoni dake da niyyar taimakawa kasar, wajen samar mata riga kafin COVID-19, da su gabatar da takardunsu. Matakin dake nuna aniyar kasar ta ci gaba da shirinta na sayen riga kafi ta hannu masu samarwa.

Ma’aikatar lafiyar ta ce, ana gudanar da shirin samar da riga kafin ne, kamar yadda manufar kula da harkokin saye-saye ta kasar ta tanada, tana mai cewa, manufar kasar ita ce, yiwa tsakanin kaso 60 zuwa 80 na al’umar kasar riga kafi, a kokarin da take na ganin ta yiwa adadin da ake bukata riga kafin cutar.

Ta kara da cewa, alluran riga da kasar ta samu karkashin nan na COVAX, zai ishi kaso 20 cikin 100 na ‘yan kasar ne kawai. Hakan na nufin cewa, dole ne ta nemo ragowar kaso 60 na alluran riga kafin daga wasu kafofi. (Ibrahim)