logo

HAUSA

Namibia ta amince da yarjejeniyar kafa hukumar sa ido kan magunguna ta Afrika

2021-02-24 11:10:05 CRI

Namibia ta zama kasa ta 5 cikin mambobin Tarayyar Afrika AU, da suka amince da yarjejeniyar kafa hukumar sa ido kan magunguna ta nahiyar Afrika (AMA).

Kasar ta kudancin Afrika, ta mika daftarin dake bayyana amincewarta ga hukumar kula da harkokin AU, inda ta zama kasa ta farko cikin mambobin kungiyar daga yankin kudancin Afrika, da ta amince da yarjejeniyar.

A cewar AU, hukumar ta AMA za ta zama hukuma ta biyu a bangaren kiwon lafiya a nahiyar, bayan Cibiyar Kandagarki da Dakile Yaduwar Cututtuka wato Africa CDC, wadda kuma za ta kara karfin kasashen da ma kungiyoyin shiyya, wajen sa ido kan harkokin da suka shafi magunguna domin kara inganci da nagarta da amincin magunguna a nahiyar.

Hukumar sa ido kan magunguna ta Afrika AMA, za ta fara aiki ne da zarar ta samu amincewar akalla kasashen nahiyar 15. (Fa’iza Mustapha)