logo

HAUSA

Namibia ta kaddamar da aikin bayar rigakafin COVID-19 da Sin ta ba ta gudunmuwarsu

2021-03-20 16:07:35 CRI

Gwamnatin Namibia ta kaddamar da aikin ba da alluran rigakafin COVID-19 a jiya Juma’a, biyo bayan isar rigakafin Sinopharm da Sin ta ba ta gudunmuwarsu.

Mataimakin ministan lafiya na kasar, Utjiua Muinjangue ne mutum na farko da ya karbi allurar a kasar, lamarin da ya kaddamar da aikin ba da rigakafin dake da nufin shafar kaso 60 na al’ummar kasar miliyan 2.5.

Matakin farko na aikin bayar da allurar zai gudana ne har zuwa ranar 19 ga watan Afrilu.

Da yake jawabi lokacin mika rigakafin a ranar Talata, jakadan Sin dake Namibia, Zhang Yiming, ya ce rigakafin shi ne makami mafi karfi na yakar kwaryar cutar, kuma ya zama mai ba da kwarin gwiwa saboda yana ceton rayuka.

Ya kara da cewa, wannan wani gagarumin ci gaba ne ga yakin da Namibia ke yi da cutar COVID-19. Kana kasar Sin na ci gaba da bayar da gudunmuwa wajen samar da rigakafin, kuma ta yi alkawarin taimakawa kasashe masu tasowa sama da 60. (Fa’iza Mustapha)