logo

HAUSA

Gwamnatin Sin Na Kokarin Kyautata Zaman Rayuwar Jama’a

2021-03-06 17:46:26 CRI

Gwamnatin Sin Na Kokarin Kyautata Zaman Rayuwar Jama’a_fororder_siin

Jiya Jumma’a 5 ga wata a nan Beijing,aka bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, inda firaministan kasar Sin Li Keqiang ya kaddamar da rahoton ayyukan gwamnati. Abubuwan da aka tanada cikin rahoton sun hada da wasu manufofi masu nasaba da zaman rayuwar jama’a, wadanda suka shafi moriyar al’umma sosai, lamarin da ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin na kokarin ganin al’ummomin kasar sun kara jin dadin zaman rayuwarsu.

Rahoton ya yi bayani da cewa, gwamnatin Sin za ta dauki matakai da za su samar da aikin yi ga mutane fiye da miliyan 11. Za ta kuma kara kokarin daidaita batun ba da ilmi ga ’ya’yan ‘yan cin rani yadda ya kamata, a kokarin ganin yara manyan gobe sun girma kamar yadda ake fata, kuma kowanensu ya samu damar yin nasara. Har ila yau gwamnatin Sin za ta ci gaba da kara kudin alawas ta fuskar kiwon lafiya da kudin Sin RMB yuan 30. Za ta kuma ci gaba da kara wa wadanda suka yi ritaya kudin fansho.

Wadannan alkaluma da firaministan kasar Sin ya ambato cikin rahoton ayyukan gwamnatin, sun bayyana dukkan abubuwan da al’ummomin kasar suka fi mai da hankali a kai. Gwamnatin Sin ta yi karin bayani sosai kan matakan da za ta dauka a bana, lamarin da ya nuna aniyarta ta daidaita batutuwan da suke biyan bukatun al’ummomin kasar yadda ya kamata. Kasar Sin tana raya kanta tare da kokarin ganin dukkan jama’arta sun ji dadin zaman rayuwarsu. Jama’ar Sin suna jin dadin zamansu saboda gwamnati tana dauka matakai filla-filla don kyautata sassa daban daban na zaman rayuwar jama’a. Rahoton ayyukan gwamnatin ya nuna aniyar gwamnatin Sin ta sanya moriyar jama’a gaba da komai. Kasar Sin ta dogaro da jama’a wajen raya kasa, ta raya kanta ne domin biyan bukatun jama’a. Don haka jama’ar kasar suna cin gajiyar ci gaban kasar. Wannan shi ne tunanin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin na tafiyar da mulkin kasa. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan