logo

HAUSA

Xi Jinping: A tabbatar da ra’ayi na al’ummar bai daya ta Sin

2021-03-06 16:16:09 CRI

Har yanzu ana ci gaba da gudanar da taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC a birnin Beijing, fadar mulkin kasar. Inda a jiya Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron tantance rahoton aikin gwamnati da tawagar wakilan jama’ar jihar Mongoliya ta Gida ta kira.

A wajen taron, shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata a yi kokarin tabbatar da amincewar jama’ar kabilu daban-daban kan kasarsu ta mahaifa, da ra’ayin samun al’ummar bai daya ta Sin, da daukaka al’adun kasar, da jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da kuma tsarin siyasa na gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin.

Dangane da dabarar raya tattalin arziki, shugaban ya bukaci jami’an jihar Mongoliya ta Gida, da su tabbatar da magance komawa yanayin fama da talauci, da raya wasu sana’o’in da jihar take da fifiko a kansu, da hada aikin kiwon dabbobi, da sana’ar yawon shakatawa, don samarwa makiyaya karin kudin shiga. Ban da wannan kuma, shugaban ya nanata muhimmancin kare muhallin jihar, don taimakawa kyautata muhallin kasar baki daya. (Bello Wang)

Bello