logo

HAUSA

Wakilan jama’ar Sin sun gabatar da shawarwari don kyautata zaman rayuwar al’umma da raya kasa

2021-03-05 15:17:13 CRI

Yau Jumma’a 5 ga wata ne aka fara zama na 4, na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 13 a nan Beijing. Shekarar bana, shekara ce da aka fara shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 14, da kuma sabon aikin zamanantar da kasar Sin ta tsarin gurguzu daga dukkan fannoni.

A daidai wannan muhimmin lokaci, taron da aka fara a yau yana da ma’ana ta musamman, wanda kuma ya jawo hankali sosai. Wakilan jama’ar kasar sun gabatar da shawarwari don kyautata zaman rayuwar al’umma da raya kasar ta Sin.

A bana kasar Sin ta samu cikakkiyar nasara wajen yaki da kangin talauci, inda aka fitar da mazauna yankunan karkara kusan miliyan 100 daga kangin talauci. Shekaru 10 ke nen kafin cimma manufar da MDD ta tsara game da rage talauci. To ko wane mataki ne kasar Sin za ta dauka a nan gaba? Kowa ya zura ido. Zhao Wanping, wani wakilin jama’a kuma mataimakin shugaban kwalejin nazarin kimiyyar aikin gona na lardin Anhui ya gabatar da wata shawara dangane da hada aikin yaki da talauci da kuma aikin farfado da yankunan karkara baki daya. Zhao ya ce, 

“A bana na gabatar da wata shawara dangane da hada aikin yaki da talauci da kuma aikin farfado da yankunan karkara baki daya. Da farko a kara kyautata da raya ababen more rayuwar jama’a a yankunan karkara. Na biyu kuma a tsara manufofi don taimakawa karin ‘yan kwadago, ta yadda za su koma yankunan karkara don su fara sana’a. Na uku kuma, na ba da shawarar karfafa gwiwar jami’ai, masana, kwararru wadanda suka yi ritaya daga aikinsu, da su ci gaba da aiki a yankunan karkara, inda za su samar da taimako ta fuskar kimiyya da fasaha ga manoma a fannin aikin gona.”

Muhimman abubuwan da aka tanada cikin manufar gwamnatin tsakiyar kasar Sin dake kan gaba su ne, farfado da yankunan karkara daga dukkan fannoni, da gaggauta zamanantar da aikin gona da kauyuka. Madam Huang Xihua, wakiliyar jama’a, kuma babbar darektar kamfanin aikin yawon shakatawa na Guangdong ta yi fatan kara azama kan farfado da yankunan karkara, ta hanyar raya aikin yawon shakatawa a yankunan karkara. Madam Huang ta ce, 

“Raya aikin yawon shakatawa yana taimakawa wajen kiyaye muhallin halittu, samun daidaito tsakanin Bil’adama da muhalli, da wadatar da mazauna yankunan karkara, da wasu sauran batutuwan da ke shafar zaman rayuwar jama’a. Alal misali, ba da ilmi ga kananan yara wadanda suke zaman gida, amma iyayensu suna aiki a sauran wurare, da kulawa da tsoffafin da suke zama a gida, amma ‘ya’yansu suna aiki a sauran wurare.”

Har ila yau, Yang Jinlong, wakilin jama’a, wanda ke koyar da sana'o'in dogaro da kai, ya nuna fatansa na ganin an kara karfin aikin koyar da sana'o'in dogaro da kai, a lokacin da ake aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 14, a kokarin horas da karin kwararru masu fasaha. 

“Ina fatan gwamnatinmu za ta kara mai da hankali kan aikin koyar da sana'o'in dogaro da kai, da sa muhimmanci kan horas da kwararrun masu fasaha. A matsayina na saurayi mai aikin fasaha, ina fatan za a kyautata matsayin masu aikin fasaha, al’ummar kasa za su girmama masu fasaha. Hakika dai, mu masu fasaha za mu kara ba da muhimmiyar gudummowa, a harkokin zaman rayuwar al’ummar kasarmu.”

A shekarun baya, aikin jigilar kaya ya samu saurin bunkasuwa a kasar Sin, wanda ya kara azama ga bunkasar wasu sana’o’i masu nasaba, da kara yin sayayya, da kara samar da guraben aikin yi, da sa kaimi kan ci gaban tattalin arziki. He Jianzhong, wakilin jama’a, kuma shugaban sashen titin Jiangping na kamfanin da ke irin wannan aiki na jigilar kayayyaki da aikewa da wasiku na Taixing, a lardin Jiangsu, ya gabatar da wata shawara dangane da kyautata tafiyar da sana’ar kai kaya, da kulawa da masu kai kaya. 

“Yanzu haka ba za a iya rabuwa da aikin kai kaya ba. Yaya za a tafiyar da sana’ar yadda ya kamata? Yaya za a kara kulawa da masu kai kaya? Ina ganin cewa, kamata ya yi gwamnatinmu, ta fito da manufa don kara kulawa da su.”

Wadannan shawarwari sun nuna yadda wakilan jama’a suke sauke nauyinsu yadda ya kamata. Wadannan shawarwari za su taiamkawa gwamnatin Sin, wajen kara saurarar ra’ayoyin jama’a, yayin da take tsara manufofin kasa. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan