logo

HAUSA

Jakadan Sin dake MDD ya yi maraba da goyon bayan kasa da kasa game da manufar kasar kan yankin HK

2021-03-06 16:18:25 CRI

Jakadan Sin dake ofishin MDD na Geneva, kana wakilin Sin a hukumomin kasa da kasa dake Switzerland, Chen Xu ya kira wani taron manema labarai a jiya, inda ya yi maraba da goyon bayan da kasashen duniya ke ba manufar kasar Sin kan yankinta na HK.

A cewar Chen Xu, yayin taro karo na 46 na kwamitin kare hakkin Bil Adama na MDD, wakilin kasar Belarus, ya gabatar da jawabi a madadin kasashe 70, inda ya nanata goyon bayansu ga manufar “kasa daya mai tsarin mulki biyu” da Sin ke aiwatarwa a yankin Hongkong. A ganin kasashen, manufar ta kawar da tashe-tashen hankali da maido da kwanciyar hankali a yankin, bayan aiwatar da dokar tsaron kasa ta Hongkong, inda kuma suka nanata adawarsu da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe masu mulkin kai, a matsayin ka’ida mai tushe na tsarin mulkin MDD, da huldar kasa da kasa.

Wakilin na Belarus ya kara da cewa, Hongkong wani yanki ne da ba za a iya rabawa da kasar Sin ba, kuma harkokin da suka shafi yankin, batutuwa ne na cikin gidan kasar Sin. Ya kuma kalubalanci bangarori daban-daban da su mutunta ikon mulkin kasar Sin da kauracewa shisshigi cikin harkokin Hongkong da sauran harkokin cikin gidan kasar Sin.

Chen Xu ya ce, wannan jawabin da wakilin Belarus ya gabatar, ya bayyana goyon bayan kasa da kasa kan matsayi da matakan da suka dace da Sin take dauka kan yankin Hongkong.

Ya kara da cewa, wasu kasashen yamma, na fakewa da batun Hongkong, suna matsawa kasar Sin lamba tare da tsoma baki cikin harkokinta na cikin gida, matakin da ba zai taba cimma nasara ba.

Bugu da kari, ya ce taro karo na 4 na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin na 13, zai tantance kudurin kyautata tsarin zabe na yankin Honkong. Kuma Sin na kalubalantar bangarorin da abin ya shafa, su nace ga tsarin mulkin MDD da ka’idar huldar kasa da kasa, don daina shisshigi cikin harkokin Hongkong da sauran harkokinta na cikin gida. (Amina Xu)