logo

HAUSA

Mahukuntan HK sun soke visar kai tsaye da ake baiwa jami’an diflomasiyya na gwamnatin Amurka

2020-12-11 13:53:21 CRI

Mahukuntan HK sun soke tsarin ba da visar kai tsaye, da ake yiwa jami’an dake dauke da fasfo na gwamnatin Amurka. Mahukuntan HK sun bayyana wannan mataki ne a daren jiya Alhamis, suna masu cewa, za a fara aiwatar da wannan mataki ne nan take.

Wannan mataki dai na zuwa ne, bayan da gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, ta ayyana makamancin wannan mataki, a matsayin ramuwa game da matakin da Amurka ta dauka kan wasu jami’an kasar ta Sin.

A cewar kakakin gwamnatin HK, karkashin wannan takunkumi, jami’an Amurka masu dauke da fasfo na gwamnati, sai sun nemi Visa kafin ziyartar yankin Hong Kong, sai dai fa idan yada zango kadai za su yi a filin jirgin yankin. Kaza lika wajibi ne su mika takardun neman visar su ga ofishin jakadanci, da na wakilcin kasar Sin, kafin samun izinin shiga yankin HK.  (Saminu)