logo

HAUSA

Sin za ta kakabawa bangaren Amurka takunkumi sakamakon tsoma baki cikin harkokin HK da Taiwan

2021-01-18 20:48:51 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce sakamakon kuskuren da Amurka ta tafka, na kakabawa wasu jami’an gwamnatin tsakiyar Sin da na yankin HK su 6 takunkumi, ita ma Sin din za ta sanyawa wasu manyan jami’an Amurka, da mambobin majalissar dokokin kasar, da wasu jami’an kungiyoyi masu zaman kansu, wadanda suka taka rawa wajen tsoma baki cikin harkokin gidan yankin HK takunkumi.

Hua wadda ta bayyana hakan a yau Litinin, lokacin da take amsa wata tambaya da aka yi mata game da wannan batu, yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa, ta ce takunkumin zai kuma shafi iyalan jami’an na Amurka.

Jami’ar ta kara da cewa, matakin Amurka na sabawa tsari, kai tsaye ya zamo tsoma baki cikin harkokin yankin HK, kana tsoma baki ne cikin harkokin gidan Sin, da ikon ta na mulkin kai, ya kuma yi matukar sabawa dokokin kasa da kasa, da ma ka’idojin cudanyar sassan kasa da kasa. Don haka Sin ke matukar Allah wadai da haka.

A wani ci gaban kuma, Sin ta kakaba makamancin wannan takunkumi kan wasu jami’an Amurka, bisa rawar da suka taka a fannin tsoma baki cikin batutuwan da suka shafi yankin Taiwan na Sin.

Uwargida Hua Chunying ta ce, matakin ya biyo bayan yadda a baya bayan nan, Amurka ta yi ikirarin sassauta togaciyar da aka yi, a bangaren musaya tsakanin Amurka da yankin na Taiwan.  (Saminu)