logo

HAUSA

Wang Wenbin: Sin na matukar adawa da duk wani mataki na tsoma baki a harkokin HK

2020-12-22 20:27:08 CRI

Kakakin ma’aikatar wajen Sin Wang Wenbin, ya ce Sin na matukar adawa da duk wani mataki na tsoma baki cikin harkokin yankin HK, da kuma baiwa masu aikata laifuka mafaka bisa dalilai na siyasa.

Wang Wenbin ya bayyana hakan ne, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da yake tsokaci game da tserewar Nathan Law zuwa Birtaniya, a gabar da ’yan sandan Hong Kong ke nemansa bisa zargin tunzura zanga-zanga.

Rahotanni na cewa a jiya Litinin, Nathan Law ya mika takardar neman samun mafakar siyasa ga mahuntan Birtaniya. (Saminu)