logo

HAUSA

Ba masu kishin kasa damar jan ragamar harkokin yankin Hongkong shi ne tushen kyautata tsarin zabe a yankin

2021-03-06 16:46:29 CRI

 

Ba masu kishin kasa damar jan ragamar harkokin yankin Hongkong shi ne tushen kyautata tsarin zabe a yankin_fororder_微信图片_20210306162751

Mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar Sin NPC, Wang Chen, ya yi bayani kan daftarin kudurin majalisar na kyautata tsarin zaben yankin Honkong, matakin da ya bayyanawa kasashen waje ka’ida mai tushe da matsayin da Sin take dauka kan wannan aiki.

Kasar Sin na yakinin cewa, tsarin ba masu kishin kasa damar jan ragamar harkokin yankin Hongkong, shi ne tushe mai dorewa na tabbatar da kwanciyar hankalin yankin. Saboda haka, bayanin Wang Chen a bikin bude majalsar NPC da aka yi jiya, ya gabatar da ka’idoji masu tushe guda 5, game da kyautata tsarin, wadanda suka hada da: nacewa ga tsarin “kasa daya mai tsarin mulkin biyu” da tabbatar da ’yan Honkong ne ke gudanar da harkokinsu da kiyaye ikon mulki da tsaro da muradun kasar Sin, sannan gudanar da harkokin HongKong bisa doka da daukar matakan dake dacewa da halin da yankin ke ciki, har ma da kara karfin gwamnatin yanki na gudanar da harkokinsa.

A nata bangaren, Jagorar yankin Hong kong Carrie Lam, ta fitar da wata sanarwa a jiya da rana, inda ta bayyana amincewa da wadannan ka’idoji biyar, tana mai cewa, gwamnatinta za ta hada kai da gwamnatin tsakiya don aiwatar da tsarin ta hanyar kafa dokokinsa. Ban da wannan kuma, bangarorin daban-daban na yankin, sun nuna goyon bayansu ga matakan da za a dauka don tabbatar da wannan tsari. (Amina Xu)