logo

HAUSA

Masanan kasa da kasa sun yabawa rawar da JKS ta taka wajen cimma nasarar kawar da talauci a Sin

2021-03-01 17:33:14 CRI

图片默认标题_fororder_微信图片_20210301164054

Masu azancin magana na cewa, “Yaro ba ta ran dare ka yi suna.” A makon da ya gabata ne kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ko kuma JKS a takaice ya gudanar da muhimmin taron murnar cikakkiyar nasarar da kasar ta cimma na kawar da talauci daga dukkan fannonin kasar ta Sin. Lamarin da ya baiwa duniya mamaki matuka. Wannan biki ya yi matukar daukar hankalin kasa da kasa duba da yadda masana ke ganin cewa a tarihin bil Adama a fadin duniya, babu wata kasa da ta iya cimma burin fitar da al’ummunta sama da miliyan 100 daga kangin talauci a cikin gajeren lokaci kamar yadda kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin ta cimma. A cikin shekaru takwas da suka gabata, a bisa kiyasi, a duk shekara Sin ta fitar da mutane miliyan 10 daga kangin talauci a cikin kasar, samun wannan nasara cikin sauri ya yi matukar burge al’ummun kasashen duniya. Koda a makon da ya gabata ma, sai dai shugaban kasar Sin Xi Jinping ya waiwayi tarihin yaki da talauci na kasar, inda ya tattara fasahohin da kasar Sin ta samu daga fannoni bakwai, dake kunshe da nacewa kan jagorancin JKS, da nacewa kan tunanin mayar da moriyar al’ummun kasa a gaban komai, da nacewa kan tsarin gurguzu mai sigar musamman na zamani. Ko shakka babu, a matsayinta na wata kasa mai tasowa mafi girma a duniya, sakamakon da kasar Sin ta samu wajen yaki da talauci, ya nuna sakamako ne da ta samu wajen kare hakkin bil Adama, matakin da zai ciyar da aikin yaki da talauci a duniya gaba. Wakilin asusun raya aikin gona na MDD dake kasar Sin Matteo Marchisio ya bayyana cewa, kasar Sin ta shaida cewa, yaki da talauci ba mafarki ba ne, kuma wannan muhimmiyar rawa ce da kasar Sin ta taka a aikin rage talauci ba ma ga kasar kawai ba har ma ga duniya baki daya. Shi ma Martin Albrow, wani shahararren masanin ilimin al’umma na kasar Birtaniya, ya bayyana wa walilin CMG a kwanan baya cewa, dalilin da ya sa jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta iya jagorantar jama’ar kasar wajen cimma nasarar kawar da talauci a kasar shi ne, domin jam’iyyar mai mulkin kasar ta dauki cikakkiyar niyyar gudanar da wannan aiki, tare da raya kasar Sin. A cewar Mista Albrow, jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ba ta taba mantawa da burtinta na bautawa jama’ar kasar ba, don haka tana iya jagorantar al’ummomin kasar wajen kokarin kawar da talauci gami da kiyaye ci gaban kasar cikin sauri. Albrow ya kara da cewa, sauran wasu manufofin da aka dauka a kasar Sin su ma sun taimaka wajen raya kasar, wadanda suka hada da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga sauran kasashe, da tsayawa kan yin hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban. (Ahmad Fagam)