logo

HAUSA

Jakadan Afganistan dake Sin: Kawar da talauci a Sin babban sakamako ne

2021-02-27 15:57:54 CRI

Jakadan Afganistan dake Sin: Kawar da talauci a Sin babban sakamako ne_fororder___172.100.100.3_temp_9500019_1_9500019_1_1_212076a9-698f-4bbe-907c-4785deb3103a

Jakadan Afganistan dake wakilci a nan kasar Sin, Javid Ahmad Qaem, ya ce kokarin da al’ummun kasar Sin suka yi a cikin shekaru takwas da suka gabata, ya cimma burin fitar da Sinawa kusan miliyan 100 daga kangin talauci cikin nasara, yana mai bayyana shi a matsayin babban sakamako da kasar Sin ta samu.

Javid Ahmad Qaem, ya bayyana haka ne a zantawarsa da wakilinmu na CMG a baya bayan nan.

Jakadan ya yi nuni da cewa, akwai daddaden zumunci a tsakanin kasashen Afganistan da Sin dake makwabtaka da juna, kuma suna da tarihin kasa mai kama da juna, shi ya sa ya dace Afganistan ta koyi fasahohin yaki da talauci irin na kasar Sin, yana mai sa ran kasashen biyu za su kara karfafa hadin gwiwa a bangaren yaki da talauci a nan gaba.(Jamila)