logo

HAUSA

Nazari na musammam ya gabatar da dabarun kasar Sin na yaki da talauci

2021-03-01 11:28:04 CRI

Gagarumar nasarar da Sin ta samu wajen yaki da talauci ya zarce dabarun da ake da su na yaki talauci, inda zai samar da sabuwar mahanga da matakai ga duniya wajen yaki da talauci.

A cewar rahoton mai taken “Nazarin Kawar da Talauci a Kasar Sin: Wata Mahanga ta siyasa da Tattalin Arziki” da cibiyar bincike ta New China Research ta kamfanin dillancin na Xinhua ta fitar, kwarewar rage talauci ta haifar da wani sabon bangaren nazari

Rahoton, wanda ya yi amfani da tunanin Shugaban kasar Xi Jinping na yaki da talauci a matsayin tubulin dabaru da akidu, ya bayyana dabarar kasar Sin na samun nasarar yaki da talauci da lalubo manufofin yakin da kuma tasirinsa ga duniya.

Ya kuma ruwaito shugaba Xi na cewa, bisa yanayin kasar da kuma kiyaye ka’idojin yaki da talauci, kasar Sin ta dauki jerin dabaru da matakai na musamman da samar da wasu jerin tsaruka da suka shafi dabaru da ayyuka da hukumomi, domin samar da wata ingantacciyar hanyar yaki da talauci da dabarar yaki da talauci mai halayyar kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)