logo

HAUSA

Masanin kasar Birtaniya: Niyyar JKS ta taka muhimmiyar rawa a kokarin cimma nasarar kawar da talauci a Sin

2021-02-28 18:54:58 CRI

Masanin kasar Birtaniya: Niyyar JKS ta taka muhimmiyar rawa a kokarin cimma nasarar kawar da talauci a Sin_fororder_0228-masani-Bello

Martin Albrow, wani shahararren masanin ilimin al’umma na kasar Birtaniya, ya bayyana wa walilin CMG a kwanan baya cewa, dalilin da ya sa jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta iya jagorantar jama’ar kasar wajen cimma nasarar kawar da talauci a kasar shi ne, domin jam’iyyar mai mulkin kasar ta dauki cikakkiyar niyyar gudanar da wannan aiki, tare da raya kasar Sin.

A cewar Mista Albrow, jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ba ta taba mantawa da burtinta na bautawa jama’ar kasar ba, don haka tana iya jagorantar al’ummomin kasar wajen kokarin kawar da talauci a kasar, gami da kiyaye ci gaban kasar cikin sauri.

Albrow ya kara da cewa, sauran wasu manufofin da aka dauka a kasar Sin su ma sun taimaka wajen raya kasar, wadanda suka hada da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga sauran kasashe, da tsayawa kan yin hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban. (Bello Wang)

Bello