logo

HAUSA

Isra’ila ta kai hari a wani yanki dake kusa da babban birnin Syria

2021-03-01 12:29:09 CRI

Isra’ila ta kai hari a wani yanki dake kusa da babban birnin Syria_fororder_1127151005_16145551325751n

Gidan talabijin na kasar Syria ya ba da rahoton wasu sabbin hare haren makamai masu linzami da Isra’ila ta kaddamar a daren jiya Lahadi a wani yanki dake daura da Damascus, babban birbin kasar.

Wata majiya daga sojojin Syria ta bayyana cewa, Isra’ila ta kaddamar da harin ne daga yankin tuddan Golan wanda ta mamaye. Rahoton ya kara da cewa, dakarun tsaron saman kasar Syria sun mayar da martani kan harin, inda suka lalata yawancin makamai masu linzamin.

Mazauna babban birnin kasar sun kalli yadda dakarun tsaron saman kasar suka dinga barin wuta a yayin da suke kokarin dakile hare haren na Isra’ila ta sararin samaniya a lokacin da aka ji mummunar karar fashewar abubuwa.

Harin na ranar Lahadi na zuwa ne kwanaki kadan bayan hare haren da Amurka ta kaddamar a wasu yankunan da mayakan dake goyon bayan Iran suke rike da shi a gabanshin Syria, lamarin da ya yi sanadiyyar kashe rayuka 22.(Ahmad)

Ahmad