logo

HAUSA

Syria ta bukaci MDD ta dakatar da hare haren Isra’ila

2020-12-31 12:00:00 CRI

Jiya Laraba ma’aikatar harkokin wajen kasar Syria ta bukaci kwamitin sulhun MDD ya dauki matakan gaggawa don dakatar da munanan hare haren da Isra’ila ke kaiwa Syria, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar na SANA ya ba da rahoto.

A sanarwar, ma’aikatar ta ce hare haren da Isra’ila ta kaddamar suna faruwa ne sakamakon goyon baya marar adadi da kasar Amurka da wasu mambobin kwamitin sulmin MDD ke bayarwa.

Kasar Syria ta sake mika bukata ga kwamitin sulhun MDD da ya yi kokarin sauke nauyin dake bisa wuyansa karkashin kundin tsarin MDD kuma abu mafi muhimmanci shi ne kokarin tabbatar da kiyaye zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, in ji sanarwar.

A ranar Laraba, an kashe wani soja guda an kuma jikkata wasu uku a sabbin hare haren makamai masu linzami da Isra’ila ta kaddamar kan sansanin sojoji dake yammacin babban birnin kasar, Damascus.(Ahmad)

Ahmad Fagam