logo

HAUSA

Kungiyar IS ta kashe sojojin Syria 6 a yankin Hamada

2021-01-04 10:38:55 CRI

Kungiyar dake sa ido kan hakkokin jama’a ta Syria, wato Syrian Observatory for Human Rights, ta ce an kashe sojojin Syria 6 yayin da wasu 8 suka ji rauni, sanadiyyar wani harin kungiyar IS a yankin Hamada dake tsakiyar kasar, a jiya Lahadi.

Kungiyar mai mazauni a Birtaniya, ta ce mayakan IS sun yi wa motar bas mai dauke da sojojin Syria, wanda ke kan hanyar Raqqa zuwa Salamiyeh, kwantar bauna.

Ta kara da cewa, bayan aukuwar harin, jiragen yankin Rasha sun yi luguden wuta a yanki, yayin da rundunar sojin kasar ta tura karin dakaru.

Kungiyar IS dai ta rasa iko da muhimman yankuna a Syria, amma mayakanta sun zabi sake hadewa tare da kaddamar da yakin sunkuru a yankin na Hamada. (Fa’iza Mustapha)